Kai Dan'adawa a Katsina, yi kokari kayi siyasa domin cimma manufar ka ta siyasa, bari kokarin neman aibun Dan'uwanka. Yin dubi iya zuwa aibu koda akwaishi batare da dubiya ba ya zuwa alkhairi hali ne na mutanen banza, hali ne na mutane marassa kishin cigaba, hali ne na mutane yan kowa ya rasa, hakakazalika, hali ne na mutanen da basa godewa aikhari. Allah yayi wadarai da mutanen da basa godewa alkhairi.
Yana daga cikin amfanin ilimi yin aiki da shi, akasin hakan manuniya ce ta rashin gishirin rayuwa. To kai, maisuka, da kiran wasu barayi, marassa ilimi, meye ribar da karibata wadda ta tunzuraka kake zagin iyayen wasu, kake cin mutuncin su, kake neman sai ka aibata su da aibun da yake naka ne wanda yake azahiri ajikin ka. Koda yake, idan kaji mutum yace wane kazane to kazan nan daya fada shi ne shi. Domin mai zuciya fara kyakkyawa, yakan alakanta mutane ne da abinda ke cikin zuciyar shi na alkhari, haka kuma abin yake ga mutumin da keda mummunar zuciya.
A koda yaushe, na kanji ba dadi, idan na karanta rubutu na kage da kushe akan Gwamnatin Jahar Katsina ko akan mutuncin wani ko Mahukantar wannan Jaha. Yana da kyau mai adawa ya nemi hujjojin sa a hannu kafin yasa alkamin sa don amayar abinda yake gani anyi ba daidai ba. Kace ance ai zancen banza ne. To waye yace? Kuma idan ance din to abisa wane dalili akace? Koko kaji suna fada, Gwamnati bata kyauta ba domin zantar da hukunci kaza. To kai ya akai kasan Gwamnati bata kyautaba baccin kaki kanemi kasan dalilin yin hakan ko kaki ka fahimci dalilan yin hakan domin wani abu na daban dake zuciyar ka.
Yana dakyau, mai rubutu ya sani, rubutu kamar zance ne domin abinda zuciya ta ayyana ma rai shi ake furzatwa a zance haka kuma abinda zuciya ta ayyana ma rai shi ake rubuta wa. To ka sani, zaka tashi gaban Allah kayi bayanin abinda bakinka ya fada, haka kaza lika, za kayi bayanin abinda hannun ka ya rubuta. Kabar yinkurin cin mutuncin wani domin cimma manufar ka ta siyasa, yin hakan aniyace makomiya.
Zai isheka misali idan kayi dubi iya zuwa baya, wasu sun samu mulki kuma wasu sun rasa hakan ya banbanta su a matsayi na rayuwa amma yau an wayi gari suna amatsayi daya na rayuwa. To kai bakatunanin cewa yau kaima Allah zai iya doraka a matsayi irin wancan, kuma baka tunanin cewa kai ma komin kokarin ka sai wani yaga gazawar ka ta wani bangaren, kada kamanta idan har Allah ya tintida ka a irin wannan matsayi to dakwai ranar da zai saukar dakai kasa. Yadda ka gudanar da tafiyar da al'amurran jama'a shine ma'aunin da zai samar ma ka da irin rayuwar da za kayi ta gaba walau mai dadi ko rashin sa.
Ina mai jan hankali ga dukkan wani mai zagi, kushe ko hassada, kiyayya da cin mutuncin shuwagabanni da ya sani shugaba jagora ne, idan ya lalace al'umma ce talalace, idan yayi nagarta al'umma ce tayi nagarta, idan yayi nasara al'umma ce tayi nasara. To kai wane irin mutun ne da bayasan gidan su da alkhairi? Ai yau da dadi ace Gwamnan garin ku yafi kowa ne Gwamna. Idan kaki Gwamna abisa kiyayya, to ka sani Allah yana sanshi shi, kuma kiyayyar mai kiyayya ba zata taba tasiri ba ga abinda yasa gaba ba, domin koba komai ya gyara tsakanin shi da Allah, yana nufin mutanen Jahar Katsina da alkhairi baya nufin zaluntar koda mutun daya tak.
Neman sani, yana daga cikin wajibci da Allah (SWA) ya wajabta ma Dan'Adam, yazo a hadissai da dama na Shugaban Tsira (SAW). Ilmin nan kau yahada da na komai; na ibada, dana rayuwa, akan komai ma yana dakyau ka nemi sani, domin isuwa ga alkhairi da guje ma cutarwa. Har lallai idan baka sani ba, to rayuwar ka tana gaf da tarko na shaidanun mutane da aljannu. Kasani cewa da ilimi ne ake sharhi akan maganganun mutane, idan baka sani ba, to ta yaya zaka yi sharhi akan maganar wani. Har idan yazama dole sai kayi sharhi a rubutu ko a maganar wani kada kayi kasa aguiwa, tambayi mai wane yake nufi da kaza domin naji ya fada ko kuma ya rubuta. Kamar yadda yake a kimiya, tunani na mutane ya bambanta kamar yadda fahimtarsu akan al'amurra ke bambanta. Wani yana fahimtar al'amurrah ne a baibai, wani kuma yana fahimtarsu a yadda suke, wani kau bayan ya fahimcesu yadda suke yana da digon basirar karin wani abu akai daidai kwatankwacin inda aka dosa da al'amari.
To kai Dan'adawa, har idan kana nufin jahar Katsina da Kasa mu Najeriya da alkhairi, kanayi ne domin cigaban al'umma ba don cigaban kanka da iyalanka ba, ga dama ta samu, zo muhadu muhada hannu da karfe domin ciyar da Jahar mu da kasar mu bakidaya izuwa gaba. Kada ka manta, yanzun ba kakar neman zabubbuka bace, kakace ta jagoranci, idan lokacin kakar neman zabubbuka tazo, lokaci ne da kowa ka iya neman jama'a ta hanyar data dace, ba irin wannan hanya ba ta cin mutuncin shuwagabanni da sauren mutane masu mutunci acikin al'ummah.
Hassan Usman Datti.
Mataimaki Akan Hanyar Sadarwa (M.A).
General Muhammadu Buhari House.
No comments:
Post a Comment